Ƴan Najeriya mata 11 da za su fafata a gasar Champions League 2026/27
Ƴan Najeriya mata 11 da za su fafata a gasar Champions League 2026/27
Daga Paris zuwa Rome da Milan da Lisbon da Sweden, ƴan wasan Najeriya mata 11 ne za su wakilci ƙungiyoyinsu daban-daban a gasar zakarun ƙwallon kafa ta ƙungiyoyin mata a Turai wato champions league ta bana.
Ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya na ci gaba da samun tagomashi, inda zaratan ƴanƙwallon tawagar ke nuna ƙwanji a manyan ƙungiyoyi a ƙasashen duniya, wanda hakan ya sa suke ƙara ɗaga tutar ƙasar.
A kakar bana, akwai aƙalla ƴanwasa mata 11 ƴan Najeriya da za su fafata a gasar UEFA Women's Champions League.
Ƴanwasan za su kasance a cikin manyan ƙungiyoyi biyar daga ƙasashe huɗu: Paris Saint-Germain ta Faransa da AS Roma da Inter Milan na Italiya da Benfica ta Portugal sai BK Häcken ta Sweden.
A sabon tsarin gasar, ƙungiyoyi 18 ne ke cikin matakin rukuni, inda kowace kungiya za ta buga wasanni shida da abokan hamayya daban-daban wato uku a gida da uku a waje.
Ƙungiyoyi huɗu na farko za su tsallaka kai tsaye zuwa wasan kusa da na kusa da ƙarshe, yayin da waɗanda suka zo daga matsayi na biyar zuwa na 12 za su fafata a kifa ɗaya ƙwala.
Ga Æ´anwasan Najeriya da za su buga gasar ta bana.
Jennifer Echegini — Paris Saint-Germain
Jennifer Echegini tana daga cikin taurarin Najeriya da suke tashe a yanzu a cikin ƴanƙallon Najeriya mata.
Ƴar wasan tsakiyar fili ce da ta ƙware wajen raba ƙwallo da kai hari, kuma ta shahara saboda ƙwarewa wajen kutsawa da ƙwallo cikin layin 18, da taimakawa a zura ƙwallo, da ma zura ƙwallon.
Echegini ta fara ƙwallon ƙafa tana jami'a a Amurka kafin ta koma Turai, inda ta buga wa Juventus ta Italiya wasa. Daga baya ta koma Paris Saint-Germain, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin mata na Faransa.
PSG za ta kara da Bayern Munich, Juventus da OH Leuven a gida, sannan ta je wajen Chelsea, Real Madrid da Manchester City.
Rasheedat Ajibade — Paris Saint-Germain
Rasheedat Ajibade, wadda magoya baya suka fi sani da "Magic", tana daga cikin fitattun Æ´an wasan Najeriya mata, kuma ita ce kyaftin É—in tawagar Super Falcons ta Najeriya.
Ta fara harkar ƙwallon ƙafa a Najeriya kafin ta koma Turai, inda ta buga wasa a Norway sannan daga baya ta yi suna sosai tare da Atletico Madrid ta Spain kafin ta koma PSG ta Faransa.
Ita ma dai za ta kara ne da ƙungiyoyin da Echegini za ta kara da su a ƙungiyar ta PSG ta Faransa.
Oluchi Basil — Paris Saint-Germain
Oluchi Basil tana cikin sabbin ƴan wasan Najeriya da ke jan hankalin masu bibiyar ƙwallon mata.
Matashiyar Æ´ar wasa ce mai shekara 16, wadda PSG ta É—auka, kuma ake ganin za ta taka rawar gani.
Ana ganin za ta ƙara samun gogewa matuƙa a yanzu da za ta wakilci ƙungiyar PSG, sannan za ta kasance tare da ƴan Najeriya biyu waɗanda suka yi suna a ƙungiyar.
Shukurat Oladipo — AS Roma
Shukurat Oladipo tana daga cikin Æ´an wasan Najeriya da za su samu damar kasancewa cikin Æ´anwasan AS Roma a wannan gasar ta zakarun turai ta mata ta bana.
Roma na daga cikin ƙungiyoyin da suke da ƙara ƙarfi a ƙwallon ƙafa ta mata a Italiya musamman a cikin ƴan shekarun nan.
Oladipo ce ta lashe kyautar ƴar wasan baya mafi ƙwazo a ƙungiyar a kakar bara, sannan ta taka rawar gani a gasar WAFCON ta Afirka.
Roma za ta karɓi baƙuncin Barcelona, Real Madrid da Servette, sannan ta je wajen Chelsea, Benfica da OH Leuven.
Rinsola Babajide — AS Roma
Rinsola Babajide tana daga cikin ƴan wasan Najeriya masu gogewa a ƙwallon ƙafa a Turai.
An haife ta a Ingila, kuma ta taso cikin tsarin ƙwallon ƙafa na ƙasar, inda ta wakilci Ingila ɗin a gasannin ƙwallon matasan ƴanƙwallo kafin daga baya ta zaɓi komawa wakiltar Najeriya.
Ta buga wa ƙungiyoyi da dama wasa a Ingila da Spain, inda ta samu gogewa a manyan gasani.
Babajide Æ´ar wasan gaba ce mai iya taka leda, inda take buga wasa ta gefen hagu
da ɓangaren dama.
Toni Payne — Inter Milan
Toni Payne tana daga cikin Æ´an wasan Najeriya masu iya taka leda a wurare daban-daban.
An haife ta a Amurka, kuma ta taɓa wakiltar ƙasar a matakin ƴanwasa matasa kafin daga baya ta zaɓi komawa wakiltar Najeriya.
Ta samu ƙwarewarta ce a Turai, inda ta taka leda a wasu manyan ƙungiyoyi musamman zamaninta a Spain, inda ta buga wa ƙungiyar Sevilla, sannan ta buga Ajax a Netherland da Everton a Ingila.
Payne tana iya taka leda a matsayin Æ´ar wasan gaba ko a gefe, ko kuma a tsakiya.
Wannan iya taka leda a wurare daban-daban na daga cikin abubuwan da ke ƙara mata muhimmanci a ƙungiyarta.
Inter za ta buga a gida da: Arsenal da Häcken da Manchester City, sannan za ta je gidan OL Lyonnes da Real Madrid da Austria Wien.
Joy Omewa — BK Häcken
Joy Omewa tana daga cikin matasan Æ´an wasan Najeriya mata masu tasowa da suka fara jan hankali saboda rawar da take takawa.
Ƴar wasan gaba ce mai iya amfani da gudunta da karsashi wajen tayar da hankalin ƴan wasan bayan abokiyar hamayya.
Kasancewarta tare da BK Häcken na ba ta damar taka leda a cikin ƙungiyar da ke cikin manyan ƙungiyoyin mata na Sweden.
Champions League na iya zama wata muhimmiyar dama gare ta wajen ƙara bayyana kanta a gaban duniya.
Häcken za ta karɓi baƙuncin Chelsea da Juventus da Manchester City, sannan ta je gidan OL Lyonnes da Paris FC da Inter Milan.
Halimatu Ayinde — BK Häcken
Halimatu Ayinde tana daga cikin Æ´anwasan Najeriya mata da suka daÉ—e ana damawa da su.
Ƴar wasan tsakiyar fili ce, kuma ta shahara da ƙwarewa wajen tare tsakiyar fili da kwantar da wasan, ga kuma ƙarfi da iya ƙwato ƙwallo.
A gasar da za a fuskanci ƙungiyoyi irin su Chelsea da Juventus da Manchester City da OL Lyonnes, gogewar Ayinde na iya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da Häcken za ta dogara da su.
Flourish Sabastine — Benfica
Flourish Sabastine tana daga cikin sabbin Æ´an wasan Najeriya da ake sa ran za su maye gurbin waÉ—anda shekarunsu suka ja.
Ƴar wasa ce mai shekara 21 da ta koma Benfica ta Portugal domin cigaba da taka leda, bayan ta buga ƙwallo a wasu ƙungiyoyin turai, irin su Galatasary da Fenerbahche duk a Turkiyya.
Benfica za ta fafata da Bayern Munich da Roma da Austria Wien a gida, sannan ta je gidan Arsenal da Juventus da HB Køge.
Janet Akekoromowei — Benfica
Ita ma Janet Akekoromowei matashiyar Æ´ar wasa ce da a yanzu ne ta fara tashe a duniyar tamaula.
Benfica ta sanar da ɗaukarta a watan Yulin 2026, inda ƴar wasan gaba mai shekara 18 ta sanya hannu a kwantiragin da zai kai zuwa 2028, tare da damar ƙara wasu shekara biyu.
Janet ƴar wasa ce da ƙungiyar Asisat Oshoala Academy ta yaye, kuma ta buga wa Najeriya a matakin ƴan ƙasa da shekara 20.
Tosin Demehin — Benfica
Tosin Demehin tana daga cikin Æ´an wasan Najeriya da ake ji da su a yanzu, inda ta kasance cikin Æ´an wasa 11 da ke yawan fara wasa.
Ta koma Benfica ne bayan ta bar ƙungiyar Galatasary a ƙarshe kakar baɗi, inda take sa ran buɗe sabon babi a ƙungiyar ta Portugal.
Benfica za ta samu ƙalubale daga ƙungiyoyi irin su Bayern Munich da Roma da Arsenal da Juventu.
How it works
Once you click Generate, Ollama reads this article and crafts 5 comprehension questions. Your answers are graded against the article content — general knowledge won't be enough. Score 70+ to count toward your certificate.
Questions are cached — you'll always get the same 5 for this article.