Ya kamata a kawo Ćarshen yaĆin Iran a yanzu
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/8/2026
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maĆwaftan Ćasashe da kuma sauran sassan duniya na ranar Juma'a 21 ga watan Agustan 2026.
Ćasashen Musulmi 8 sun yi alawadai da shirin Israâila na gina matsuguni a Yammacin Kogin Jordan
Ćasashen Musulmi guda takwas sun fitar da sanarwar haÉin gwiwa inda suka yi Allah-wadai da manufofin Israâila na gina matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan.
Ministocin harkokin wajen Ćasashen da suka haÉa da Pakistan, Masar, Indonesia da Saudiyya sun yi watsi da shirin gina sabon babban matsugunin E-1, suna cewa hakan na iya Ćara rura wutar rikici.
Shirin gina matsugunin ya kuma fuskanci suka daga wasu Ćasashe saboda muhimmancin yankin da ake son gina shi, wanda ke tsakanin gabashin birnin Kudus da sauran sassan Yammacin Kogin Jordan.
Sinadaran gina jiki 5 da mata ke buĆata
Cin abinci mai gina jiki da kuma daidaitaccen tsari shi ne ginshiĆi mafi muhimmanci na lafiyar jiki. Saboda haka, irin zaÉin abincin da kike yi yana da babban tasiri ga Ćoshin lafiyarki da kuma yadda za ki tsufa cikin koshin lafiya.
Haka kuma, matakai daban-daban na rayuwar mace, kamar lokacin al'ada, daukar ciki, da kuma lokacin daina jinin al'ada (menopause), suna sauya buĆatarta ga wasu muhimman sinadaran gina jiki.
Da wannan a zuciya, mun bayyana muhimman sinadaran gina jiki guda biyar da kowace mace take buĆata.
Ci gaba da karantawa domin Ćarin bayani. Haka kuma, za ki iya duba abincin da ke da wadataccen Ćarfe (iron), abincin da ke da yalwar zaruruwa (fiber), da kuma shawarwari kan yadda za a samu ciki cikin koshin lafiya.
Zafin El NiĂąo na iya Ćara munin da ba a taÉa gani ba - Masana
Masana yanayi sun yi gargadin cewa yanayin zafinn El NiĂąo da ke tasowa a tekun Pacific a bana na iya zama mafi muni da aka taÉa gani cikin sama da shekara 100.
El NiĂąo wani yanayi ne da ke faruwa lokaci-lokaci, inda yanayin ruwan tekun Pacific ke Ćara Éumi fiye da yadda aka saba, lamarin da ke sauya yanayin ruwan sama da zafi a sassa daban-daban na duniya.
Masana kimiyya sun ce yanayin zafin ruwan tekun Pacific a bana na iya Ćaruwa da kusan maki huÉu, abin da ka iya sa wannan El NiĂąo ya yi tsanani sosai.
Tuni aka fara ganin tasirinsa a wasu sassan duniya. A Indiya, an samu Ćarancin ruwan sama fiye da yadda aka saba, yayin da Peru ke fama da ambaliyar ruwa.
A Panama kuma, Ćarancin ruwan sama ya rage yawan jiragen ruwa da ke amfani da Mashigar Ruwan Panama, wadda muhimmiyar hanya ce ta safarar kayayyaki tsakanin tekuna.
Masana sun kuma yi gargadin cewa El NiĂąo na iya Ćara tsananta fari a dazukan Amazon da wasu sassan Australia, yayin da a wasu sassan duniya zai iya haifar da Ćarin ruwan sama da guguwa.
Barkewar cutar Ebola na Ćara tsananta a Kongo â MDD
Babban jamiâin Majalisar Ćinkin Duniya mai kula da yaĆi da cutar Ebola, Julien Harneis, ya yi gargadin cewa barkewar cutar a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo na Ćara tsananta cikin sauri.
Ya ce rabin cikin mutane 2,500 da suka mutu sakamakon cutar, sun rasu ne cikin kwanaki 20 da suka gabata.
Harneis ya ce cutar na yaÉuwa cikin sauri zuwa wurare da dama, lamarin da ya fi Ćarfin ĆoĆarin da ake yi na dakile ta.
Ya ce ana buĆatar Ćarin maâaikata da kayan aiki a yankunan gabashin Kongo domin rage yaÉuwar cutar.
A gefe guda, Ćungiyar agaji ta Save the Children ta ce aĆalla yara 180 ne suka rasa iyayensu ko masu kula da su tun bayan barkewar cutar a watan Mayu.
An mayar da Imran Khan gidan yari bayan duba lafiyarsa
An mayar da tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan, gidan yari bayan an kai shi asibiti domin duba lafiyarsa a Islamabad.
Likitocin gwamnati sun ce yana cikin Ćoshin lafiya, sai dai jamâiyyarsa ta zargi hukumomi da karya umarnin Kotun Koli, bayan da aka kai shi asibitin gwamnati maimakon wani asibiti mai zaman kansa da kotun ta bayar da umarnin a kai shi.
Jamâiyyar ta ce an mayar da Mista Khan gidan yari cikin saâoâi kaÉan, kuma tana shirin shigar da Ćara kan zargin raina umarnin kotun.
Tun shekarar 2023 ake tsare da Imran Khan a gidan yari kan zarge-zargen da ya ce ana yi masa ne saboda adawar siyasa.
Ya kamata a kawo Ćarshen yaĆin Iran da Amurka a yanzu - Pezeshksian
Shugaban
Ćasar Iran Masoud Pezeshksian ya ce lokaci ya yi da za a kawo Ćarshen yaĆin da
Ćasar ke yi da Amurka kasancewar a yanzu Iran Éin ce a âsamaâ.
Pezeshksian
ya ce: âyanzu ne ya fi cancanta a kawo Ćarshen yaĆin, yayin da muke da tasiri,
muke da sauran mutunci kuma duk duniya aka amince cewa mun yi nasara, sannan ya
jaddada cewa Amurka ta saÉa wa dokoki ta hanyar kai hare-hare kan makarantu da
asibitoci da kayan amfanin alâumma, âkuma duniya ta tsane ta.â
Pezeshksian
ya soki lamirin waÉanda ya ce âba su san abin da yake faruwa baâ kuma ba su san
halin da gwamnati da kwamandojin sojin Ćasar da majalisar dokoki ke ciki ba.
Suna magana ba tare da sanin wahalar da ake ciki ba.â
Sai
dai shugaban ya ce kalamansa ba suna nufin miĆa wuya ba ne: âBa za mu miĆa wuya
ba ta kowane irin fanni, babu tantama a kan hakan. Za mu tunkare su har lokacin
da numfashinmu zai fita kuma za mu azabtar da su.â
Kalaman
na shugaban Iran na zuwa ne yayin da gwamnatin Amurka ke sauya salon yaĆin,
inda a yanzu take Ćokarin komawa kan matsi na tattalin arziĆi.
Mace mafi tsufa a duniya na bikin zagayowar ranar haihuwarta
Bilâadama mafi tsufa a duniya na cika shekara 117 a duniya yau Jumaâa. Dattijuwar ta yi
bikin ne a cikin iyali da abokan arziĆi.
Ethel
Caterham wadda ke zama a gidan kula da tsofaffi na Hallmark Lakeview da ke
Surrey a Birtaniya.
An
haife ta shekara uku gabanin hatsarin jirgin ruwa na Titanic kuma shekara
takwas gabanin juyin juya halin Rasha, haka nan ta shaida yaĆin duniya na farko
da na biyu.
Haka
nan kuma tana cikin mutane mafiya tsufa da suka tsallake annobar korona, inda
kamu da cutar a shekarar 2020 saâilin tana da shekara 110 a duniya, a cewar kundin
bajinta na Guinness.
Ethel ita ce Ć´ar'auta a gidansu, inda iyayenta ke da Ć´aĆ´a 9.
Matar wadda ta riĆa tuĆa mota har a lokacin da take da shekara 97, ta karÉi baĆuncin Sarki Charles a watan Satumban bara, jim kadan bayan bikin cikar ta shekara 116 da haihuwa.
Lokacin ziyarar ta tuno masa abin da ya faru a lokacin da aka naÉa shi sarautar Yariman Wales a shekarar 1969, lokacin yana da shekara 21.
Ta ce: âKowace budurwa a lokacin tana son ka, kowa na son ya aure ka.â
Sai dai har yanzu wata Bafaranshiya Janne Calment ce ke riĆe da kambin bilâadama mafi tsufa a duniya, inda ta rasu a shekarar 1997 lokacin tana da shekara 122 da kwana 164, a cewar kambin tarihi na Guinness.
Yadda Ebola ke mayar da yara marayu a Kwango
Wani sabon rahoton da Ćungiyar kula da yara ta Save the Children ta fitar ya ce aĆalla yara 180 a Jamhuriyar DimokuraÉiyyar Kwango ne suka rasa uwa da uba ko kuma Éaukacin masu kula da su sanadiyyar Éarkewar cutar Ebola tun daga watan Mayu.
Hukumomi a lardin Ituri, inda nan ne cibiyar yaÉuwar cutar sun ce an kuma raba yara sama da 100 sanadiyyar karÉar magani.
Ćungiyar ta nuna damuwa kan cewa yaran da abin ya shafa na cikin haÉarin fuskantar cin zarafi da kuma shiga cikin damuwa.
A yanzu Ćungiyar ta samar da wuraren kulawa da irin waÉannan yara yayin da iyayensu ke karÉar magani.
Cutar na ci gaba da yaÉuwa cikin sauri, inda aka samu sama da mutum 5,000 da suka harbu.
Mutum takwas sun mutun bayan jirgi ya faÉi a sansanin sojin Amurka
Rundunar sojin saman Amurka ta ce mutum takwas sun mutu bayan wani jirgin sama da ke aiki da rundunar ya fadi a jihar Alaska.
Jirgin wanda wani kamfanin farar hula ke aiki da shi Ćarkashin wani kwantiragi da gwamnati ya faÉi ne da rana a kusa da Cape Newenham a yankin Anchorage.
Hukumomi sun ce har yanzu ba a bayyana mutanen da ke cikin jirgin ko kuma manufar tafiyarsu ba.
Shugaban rundunar sojin saman Amurka a Alaska, Laftanar Janar Robert Davis, ya bayyana waÉanda suka mutu a matsayin Ćwararru masu sadaukar da kai da ke gudanar da wani muhimmin aiki a wani yanayi mai matuĆar wahala.
"Wannan babban rashi ne mai raÉaÉi ga iyalan sojinmu da kuma alâummomin da muke yi wa hidima," in ji Davis a cikin wata sanarwa.
Ya Ćara da cewa babban abin da suka fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne tallafa wa iyalan waÉanda suka mutu da kuma abokan aikinsu a wannan lokaci na jimami.
A cewar rundunar sojin saman Amurka da ke Alaska, jirgin ya tashi ne daga babban filin jirgin sama na Anchorage zuwa Cape Newenham, mai nisan kusan kilomita 725 daga birnin Alaska.
Masu aikin ceto da suka isa wurin da hatsarin ya auku sun tabbatar da cewa babu wanda ya tsira.
An fara bincike domin gano musabbabin hatsarin, yayin da hukumomi suka ce za a bayyana sunayen mamatan ne bayan an sanar da iyalansu.
Zan kai wa Iran hari a kowane lokaci matuĆar akwai buĆatar hakan â Trump
Shugaban
Amurka Donald Trump ya ce zai iya kai wa Iran hari ko sau 100 ne domin ganin ya
hana Ćasar mallakar makamin nukiliya.
A wata
tattaunawa ta rediyo, Trump ya ce in ban da matakin da ya Éauka, da yanzu babu
Israâila ko Ćasashen Gabas ta Tsakiya.
A
cikin tattaunawar Trump ya ce ya bayar da umarnin kai wa Iran hari ne yayin da bai
wuce mako biyu ta mallaki makamin nukiliya ba.
Trump
ya ce duk da irin labaran da ake yaÉawa amma Amurka ce ke iko da mashigar
Hormuz.
Ya
kuma dage kan cewa an yi matuĆar illa ga Éangaren makamai masu linzami da kuma
na jirage marasa matuĆa na Ćasar ta Iran, yayin da aka yi matuĆar raunana
tattalin arziĆinta.
Mutanen da suka mutu a haÉarin kwale-kwale a Sokoto sun kai 48
Kimanin
mutum 48 ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman yara 12 bayan haÉarin
jirgin ruwa da ya faru a yankin Goronya da ke jihar Sokoto.
Akasarin
waÉanda lamarin ya rutsa da su yara ne waÉanda ke kan hanyar zuwa gona a safiyar
jiya Alhamis.
A
tattaunawarsa da BBC, Éan majalisar tarayya mai wakiltar Gada da Goronyo a
majalisar wakilan Najeriya Bashir Gorau ya ce a halin yanzu masu ninkaya na
ci gaba da aikin ceto domin ganin ko za a samo sauran yaran da suka Éace da
ransu.
âAkasarin
waÉanda abin ya rutsa da su yara ne da mata, yara Ć´an Ćasa da shekara 10,â a
cewar Gorau.
âRafi
ya raba mutanen Ćauyen da gonakinsu, shi ya sa a kodayaushe mutane ke amfani da
kwale-kwalen katako domin zuwa gona,â kamar yadda Éan majalisar ya yi Ćarin
haske.
A Najeriya
ana yawan fuskantar hatsarin kwale-kwale wanda ke laĆume rayuka musamman a
yankunan karkara.
Lamarin
ya fi Ćamari ne a lokacin damina, inda rafuka kan cika da ruwa, sannan kuma babu
wasu matakan kariya da ake amfani da su wajen irin wannan sufuri, haÉi da
rashin ingancin kwale-kwalen.
Iyayen yara sun yi zanga-zanga a Borno
Iyayen yaran da aka sace a jihar Borno da ke arewa maso yammacin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a garin Uba jiya Alhamis domin neman gwamnati ta ceto kusan yara 100 da ake garkuwa da su daga yankin.
A ranar 15 ga watan Mayu ne wasu mahara da ake zargin mayaĆan Boko Haram ne suka kai farmaki a wata makaranta da ke Ćauyen Mussa mai maĆwaftaka da dajin Sambisa, inda suka sace Éalibai kimanin 45 cikin har da Ćananan yara, wadanda har yanzu suke hannun Ć´an bindiga.
Zanga-zangar ta nuna yadda iyaye ke cikin damuwa kan yawaitar garkuwa da mutane da kuma hare-haren Ćungiyar Boko Haram duk da kasancewar sojoji a yankin.
ISWAP da Boko Haram sun riĆa kai hare-hare da sace Éalibai a makarantun yankin tsawon sama da shekara 15.
Baya ga satar Éaliban na Ćauyen Mussa, an kuma kai hari a wata makaranta a Ćauyen Lassa mai maĆwaftaka ranar 29 ga watan Yuni inda aka sace Éalibai 36 da kuma malami waÉanda su ma har yanzu suna hannun masu garkuwa da su.
A watan da ya gabata ne hukumomin Ćasar suka karÉo Éalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jiyar Oyo da ke kudu maso yammacin Ćasar.
Japan ta zartar da hukuncin kisa karo na farko cikin shekara Éaya
Japan ta aiwatar da hukuncin kisa na farko cikin sama da shekara guda.
An yanke wa Sunayo Takami hukuncin kisa ne bayan samun shi da laifin kashe mutane biyar a wani hari da aka Ćona wani wurin wasa a shekarar 2009.
Hakan na zuwa ne bayan shekaru 17 da aikata laifin, kuma shi ne na farko tun bayan zuwan wannan gwamnatin mai ci.
Japan na daya daga cikin kasashe biyu kacal, wato ita da Amurka da ke cikin kungiyar G7 da ke aiwatar da hukuncin kisa, amma ba kasafai take aiwatar da shi ba.
Barka da warhaka!
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'a a wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maĆwaftanta da kuma sassan duniya.
Za ku iya leĆawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.
How it works
Once you click Generate, Ollama reads this article and crafts 5 comprehension questions. Your answers are graded against the article content â general knowledge won't be enough. Score 70+ to count toward your certificate.
Questions are cached â you'll always get the same 5 for this article.