tech_surveillance1322 wordsRead on Arc Codex

Yadda matakin ĆŠangote na sayar da man fetur a dala zai shafe ku

Yadda matakin Ɗangote na sayar da man fetur a dala zai shafe ku Matakin da kamfanin Ɗangote ya ɗauka na fara sayar da man fetur da dala maimakon naira ya janyo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya da masana tattalin arziki musamman dangane da yadda zai shafi ƴan ƙasar. Kamfanin ya ce wannan sauyi na da nasaba da buƙatun kasuwanci da kuma yanayin kasuwar canjin kuɗi. Sai dai matakin ya haifar da tambayoyi kan yadda hakan zai shafi farashin fetur, darajar naira da kuma aljihun talakawan Najeriya, musamman a daidai lokacin da jama'a ke fama da tsadar rayuwa. Yayin da wasu ke ganin hakan na iya taimaka wa masana'antar mai wajen samun sauƙin gudanar da harkokinta, wasu na fargabar cewa sayar da mai da dala na iya ƙara wa 'yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta. To ko me ya sa aka ɗauki wannan mataki, kuma mene ne tasirinsa ga 'yan Najeriya? Wani masanin tattalin arziƙi, kuma malami a jami'ar Philomath, Farfesa Ahmad Adamu ya amsa waɗannan tambayoyi na BBC dangane da wannan sauyi da kuma irin tasirin da zai iya haifarwa ga tattalin arziƙin ƙasar. Me ya janyo sauyin? Masanin tattalin arziƙi, Farfesa Ahmad Adamu, ya ce matakin da Kamfanin Dangote ya ɗauka na fara sayar da man fetur da dala na da alaƙa da sauye-sauyen da suka faru a kasuwar mai a Najeriya. Ya bayyana cewa tun farko an tsara wata yarjejeniya da za ta ba matatar damar karɓar wani ɓangare na ɗanyen man fetur da take buƙata tare da biyan kuɗinsa da naira, lamarin da ya sa ita ma take sayar da tataccen man fetur a cikin ƙasa da kuɗin naira. Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku. Latsa nan domin shiga Karshen Whatsapp Sai dai Farfesan ya ce abubuwa sun sauya ne bayan raguwar shigo da man fetur daga ƙasashen waje, wanda ya sa matatar Dangote ta ƙara taka muhimmiyar rawa wajen samar da man fetur a ƙasar. "A lokacin da aka fara wannan yaƙi na Iran, shigo da man fetur Najeriya ya ragu sosai, sai ya kasance matatar Dangote ce ke samar da kusan kashi 80 cikin 100 na man Najeriya." A cewarsa, wannan sauyin ya haifar da ƙarin kuɗin naira da kamfanin ke samu daga kasuwar cikin gida, yayin da kuma yake buƙatar dala domin gudanar da wasu muhimman harkokinsa. "Yana karɓar naira yanzu fiye da yadda yake karɓa a da. Saboda haka naira ta yi masa yawa a hannu, amma shi ya fi buƙatar dala saboda akwai wasu nau'ikan ɗanyen mai da ake saya da dala." in ji Ahmad Adamu. Masanin ya ƙara da cewa ko da a cikin Najeriya ne, akwai wasu mu'amalolin da ba za a iya kauce wa amfani da dala a cikinsu ba, musamman wajen sayen wasu nau'ikan ɗanyen mai da sauran kayayyakin da ake buƙata wajen tacewa. "Akwai wasu ɓangarorin ɗanyen man fetur da dole ne a siya da dala, domin ita kanta NNPC ba za ta so a ce ba ta da dala a hannunta ba." Ya ce hakan na nufin cewa yawan dogaro da matatar Dangote wajen samar da man fetur a Najeriya ya sa kamfanin ke neman hanyoyin samun dala domin biyan wasu muhimman buƙatun kasuwancinsa. Tasirin sauyin kan ƴan Najeriya Masanin ya ce tasirin wannan sauyin zai iya ƙara jefa tattalin arziƙin Najeriya cikin matsin lamba, saboda yawan buƙatar dala na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar ƙasar. A cewarsa, duk lokacin da darajar dala ta ƙaru a kan naira, al'amuran tattalin arziƙi kan ƙara tsananta ga ƴan ƙasa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da raguwar ƙarfin saye. "Dama babban matsalar tattalin arziƙin Najeriya ita ce dala. Duk lokacin da dala ta yi tsada, tattalin arziƙin Najeriya yana ƙara ƙunci, yana ƙara raunana, sannan ƴan Najeriya suna ƙara talaucewa sakamakon hauhawar farashi." Farfesan ya ce idan aka kai ga matsayin da duk harkokin saye da sayar da man fetur za su dogara ne da dala, hakan zai ƙara yawan buƙatar kuɗin ƙasashen waje a kasuwa, lamarin da zai iya ƙara raunana naira. "Idan aka ce duk buƙatar tataccen man fetur sai an biya da dala, hakan zai ƙara yawan buƙatar dala. Wannan kuma zai ƙara rage darajar naira, sannan farashin man fetur zai riƙa ƙara tsada duk lokacin da dala ta ƙara tsada." Ya kuma bayyana cewa tasirin hakan ba zai tsaya ga manyan dillalan man fetur ba kaɗai, domin a ƙarshe kuɗin da aka kashe wajen sayen dala za a ɗora shi kan masu amfani. Farfesa Ahmad Adamu ya ce idan aka bar irin wannan yanayi ya daɗe ba tare da matakan kariya ba, zai iya ƙara jefa farashin man fetur da sauran kayayyaki cikin tashin gwauron zabo, abin da zai ƙara nauyi a kan rayuwar talakawan Najeriya. "Wannan gaskiya babbar matsala ce, domin duk wani ƙarin buƙatar dala yana da tasiri kai tsaye ga farashi da kuma rayuwar al'umma." ya ƙara da cewa Ta yaya dala za ta shafi farashin mai a Najeriya? Farfesan ya bayyana cewa a halin yanzu, idan aka yi la'akari da farashin man fetur da ake sayarwa a kasuwa da kuma darajar dala, akwai yiwuwar lita ɗaya ta yi kusan daidai da dala ɗaya idan aka yi lissafi da canjin kuɗi. "Yanzu tunda dai ana sayar da lita ɗaya na man fetur kan kusan naira 1,300, kuma kowace dala tana kan naira 1,300 ko 1,400, to za a iya cewa kowace lita tana iya kusan zama daidai da dala ɗaya," in ji Farfesa Ahmad Adamu. Sai dai ya ce wannan ba yana nufin farashin zai tsaya a nan ba, domin duk wani ƙarin hauhawar darajar dala zai iya haifar da ƙarin tsadar man fetur. "Amma nan gaba idan har dalar ta ƙara ƙaruwa, farashin man fetur ma zai iya ƙaruwa, saboda idan kuɗin da ake amfani da shi wajen saye ko samar da mai ya ƙaru, to dole hakan ya shafi farashin da mai amfani na ƙarshe zai biya," ya ƙara da cewa. Ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa ake buƙatar a kula da tsarin amfani da dala wajen harkar man fetur, domin sauyi a kasuwar canjin kuɗi na iya yin tasiri kai tsaye kan rayuwar 'yan Najeriya. Mece ce mafita? Masanin tattalin arziƙin ya ce gwamnati na da muhimmiyar rawa da za ta taka domin magance matsalar da ka iya biyo bayan matakin kamfanin Dangote na fara sayar da man fetur da dala maimakon naira. Masanin ya ce hanya ta farko ita ce gwamnati ta tattauna da matatar Dangote domin tabbatar da cewa ana ci gaba da sayar da man fetur da naira a kasuwar cikin gida. Ya bayyana cewa, idan kamfanin na bukatar dala domin gudanar da harkokinsa, gwamnati za ta iya taimaka masa ta hanyar samar da kuɗaɗen waje, yayin da kamfanin zai riƙa sayar da man fetur ga 'yan Najeriya da naira. Masanin ya ce hakan zai taimaka wajen rage matsin lamba kan masu amfani da man fetur, musamman a lokacin da darajar naira ke fuskantar kalubale a kasuwar canji. Ya kara da cewa, gwamnati na da damar amfani da dalolin da take da su domin rage yawan sayen man fetur da ake yi da kuɗin waje. "Tunda gwamnati tana da daloli a hannunta yanzu, za ta iya amfani da su wajen rage sayen man fetur a Najeriya da ake yi da dala, ta hanyar sayen duk nairan da aka sayar da dala." Ya kuma ce wani mataki da gwamnati za ta iya dauka shi ne bayar da wani tallafi na wucin gadi ga masu sayar da man fetur domin rage yiwuwar tashin farashin man a kasuwa. A cewarsa, duk da cewa irin wannan tallafi na iya saɓawa wasu manufofin gwamnati na dogaro da kasuwa, akwai lokutan da ake bukatar ɗaukar matakin gaggawa domin kare al'umma. Masanin ya ce ya kamata gwamnati ta duba duk hanyoyin da za su taimaka wajen kare masu amfani da man fetur daga ƙarin tsadar rayuwa da ka iya biyo bayan sauyin tsarin sayar da man.

How it works

Once you click Generate, Ollama reads this article and crafts 5 comprehension questions. Your answers are graded against the article content — general knowledge won't be enough. Score 70+ to count toward your certificate.

Questions are cached — you'll always get the same 5 for this article.